languageIcon
search
search
Zikirin Dare Da Yini Zikirin Dare Da Yini ( Adadinsu 4 Babuka )

1 Sau Da Yawa

brightness_1

أَمْسَيْنَا وَأَمْسَى الْمُلْكُ لِلَّهِ، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ خَيْرِ هَذِهِ اللَّيْلَةِ وَخَيْرِ مَا فِيهَا، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا وَشَرِّ مَا فِيهَا، اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْكَسَلِ، وَالْهَرَمِ، وَسُوءِ الْكِبَرِ، وَفِتْنَةِ الدُّنْيَا، وَعَذَابِ الْقَبْرِ

“Amsainá wa amsal- mulku lilláhi, wal hamdu lilláhi láiláha illalláhu wahdahu lá sharíka lahú. Alláhumma inní as’aluka min khairi házihil- lailah wa khairi má fíhá, wa aúzu bika min sharrihá wa sharri má fíhá. Alláhumma inní a’úzu bika minal- kasali, wal- harami, wa sú’il kibari, wa fitnatid- duniyá, wa azábil qabri.”  (Mun maraita kuma mulkiya maraita a hannun Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai; bas hi da abokin tarayya. Ya Ubangiji! Ina roqonka alhairi duk da wannan dare yake tare da shi, da wanda yake cikinsa. Ina kuma neman tsari daga sharrin da yake tare da shi, da wanda yake cikinsa. Ya Ubangiji! Ina kuma neman tsarinka daga matsalar kasala, da ta tsufa, da ta girmann kwabo, da fitnar duniya, da kuma a zabar qabari.” Idan kuma ya wayi gari, sai ya sake karanta wannan zikiri, yana mai cewa: “Asbahná wa asbahal mulku lilláhi….as’aluka khaira má fí hazal- yaumi wa khaira má ba’adahú, wa aúzu bika min sharri má fí házal- yaumi wa sharra má ba’adahú…” (Mun wayi gari kuma mulki ya wayi gari a hannun Allah… ina roqon ka alhairin da yake cikin wannan yini, da wanda yake bayansa. Ina kuma neman tsarinka daga sharrin da yake cikin wannan yini, da wanda yake bayansa.) [Muslim:2723]

.......

1 Sau Da Yawa

brightness_1

اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ خَلَقْتَنِي، وَأَنَا عَبْدُكَ، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ، وَأَبُوءُ لَكَ بِذَنْبِي فَاغْفِرْ لِي فَإِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ

Shugaban Dukan Istigfári: “Alláhumma anta Rabbí, lá’iláha illáh anta, halaqtaní, wa aná abduka, wa ana alá wa’adika mastaxa’atu. A’úzu bika min sharri má sana’atu, wa abú’u bika bi ni’imatika alayya, wa abú’u laka bi zambí, fagfir lí fa’innahú lá yagfiruz-zunúba illá anta.”  (Ya Ubangiji! Kai ne abin bautata, babu wani abin bauta da gaskiya sai kai. Kai ka halicce ni; ni bawanka ne, ina kuma nan a kan alqawali da yarjejeniyar da take tsakanina da kai gwargwadon ikona. Ina neman tsarinka daga sharrin abin da na aikata. Ina godiya a kan ni’imar da ka yi mani, ina kuma yi maka iqirarin ayyuka na na zunubi tare da roqon ka yi mani gafara, domin babu wanda yake gafarta zunubai sai kai.) Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Duk wanda ya karabta wannan addu’a da rana, yana mai cikakken imani da ita. Idan Allah ya karvi rayuwarsa a wannan rana, kafin marece, to, ko shakka babu yana daga cikin ‘yan Aljanna. Wanda duk kuma ya karanta ta a cikin dare, yana mai cikakken imani da ita. Idan Allah ya karvi rayuwarsa kafin a wayi gari, to, yana daga cikin ‘yan Aljanna.” (Buhari:6306)  

.......

1 Sau Da Yawa