10 Sau Da Yawa
لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
“Duk wanda ya faxi: Lá’iláha illalláh wahdahú lá sharíka lahú, lahul- mulku wa lahul- hamdu, wa huwa alá kulli shai’in Qadírun.” ((Babu abin bauta da gaskiya sai Allah shi kaxai; ba shi da abokin tarayya. Mulki da godiya duka sun tabbata gare shi, mai iko ne kuma shi a kan komai.) “Duk wanda ya karanta waxannan lamomi qafa goma a lokacin da ya wayi gari, za a rubuta masa lada xari xaya a sanadiyyarta, a kuma wanke masa zunubi xari xaya, a kuma rubuta masa lada daidai da ta wanda ya ‘yanta kuyanga, a kuma bas hi cikakken tsaro a cikin wannan yini tun daga farkonsa har qarshe. Wanda kuma duk ya karanta ta qafa xari xaya xin, zai samu kwatankwacin wancan sakamako.” (Ahmad:8719), Malam Ibn Báz kuma rahimahullahu ta’alah, ya kyautata danganensa
1 Sau Da Yawa
أَمْسَيْنَا وَأَمْسَى الْمُلْكُ لِلَّهِ، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ خَيْرِ هَذِهِ اللَّيْلَةِ وَخَيْرِ مَا فِيهَا، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا وَشَرِّ مَا فِيهَا، اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْكَسَلِ، وَالْهَرَمِ، وَسُوءِ الْكِبَرِ، وَفِتْنَةِ الدُّنْيَا، وَعَذَابِ الْقَبْرِ
“Amsainá wa amsal- mulku lilláhi, wal hamdu lilláhi láiláha illalláhu wahdahu lá sharíka lahú. Alláhumma inní as’aluka min khairi házihil- lailah wa khairi má fíhá, wa aúzu bika min sharrihá wa sharri má fíhá. Alláhumma inní a’úzu bika minal- kasali, wal- harami, wa sú’il kibari, wa fitnatid- duniyá, wa azábil qabri.” (Mun maraita kuma mulkiya maraita a hannun Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai; bas hi da abokin tarayya. Ya Ubangiji! Ina roqonka alhairi duk da wannan dare yake tare da shi, da wanda yake cikinsa. Ina kuma neman tsari daga sharrin da yake tare da shi, da wanda yake cikinsa. Ya Ubangiji! Ina kuma neman tsarinka daga matsalar kasala, da ta tsufa, da ta girmann kwabo, da fitnar duniya, da kuma a zabar qabari.” Idan kuma ya wayi gari, sai ya sake karanta wannan zikiri, yana mai cewa: “Asbahná wa asbahal mulku lilláhi….as’aluka khaira má fí hazal- yaumi wa khaira má ba’adahú, wa aúzu bika min sharri má fí házal- yaumi wa sharra má ba’adahú…” (Mun wayi gari kuma mulki ya wayi gari a hannun Allah… ina roqon ka alhairin da yake cikin wannan yini, da wanda yake bayansa. Ina kuma neman tsarinka daga sharrin da yake cikin wannan yini, da wanda yake bayansa.) [Muslim:2723]
1 Sau Da Yawa
اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ خَلَقْتَنِي، وَأَنَا عَبْدُكَ، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ، وَأَبُوءُ لَكَ بِذَنْبِي فَاغْفِرْ لِي فَإِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ
Shugaban Dukan Istigfári: “Alláhumma anta Rabbí, lá’iláha illáh anta, halaqtaní, wa aná abduka, wa ana alá wa’adika mastaxa’atu. A’úzu bika min sharri má sana’atu, wa abú’u bika bi ni’imatika alayya, wa abú’u laka bi zambí, fagfir lí fa’innahú lá yagfiruz-zunúba illá anta.” (Ya Ubangiji! Kai ne abin bautata, babu wani abin bauta da gaskiya sai kai. Kai ka halicce ni; ni bawanka ne, ina kuma nan a kan alqawali da yarjejeniyar da take tsakanina da kai gwargwadon ikona. Ina neman tsarinka daga sharrin abin da na aikata. Ina godiya a kan ni’imar da ka yi mani, ina kuma yi maka iqirarin ayyuka na na zunubi tare da roqon ka yi mani gafara, domin babu wanda yake gafarta zunubai sai kai.) Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “Duk wanda ya karabta wannan addu’a da rana, yana mai cikakken imani da ita. Idan Allah ya karvi rayuwarsa a wannan rana, kafin marece, to, ko shakka babu yana daga cikin ‘yan Aljanna. Wanda duk kuma ya karanta ta a cikin dare, yana mai cikakken imani da ita. Idan Allah ya karvi rayuwarsa kafin a wayi gari, to, yana daga cikin ‘yan Aljanna.” (Buhari:6306)
1 Sau Da Yawa
اللَّهُمَّ بِكَ أَمْسَيْنَا وَبِكَ أَصْبَحْنَا وَبِكَ نَحْيَا وَبِكَ نَمُوتُ وَإِلَيْكَ الْمَصِير
“Idan xayanku ya wayi gari, sai, ya karanta wannan addu’a: “Alláhumma bika asbahná, wa bika amsainá, wa bika nahyá, wa bika namútu, wa ilaikan- nushúr.” (Ya Ubangiji! Da yardarka muka wayi gari, da yardarka kuma muka maraita. Da yardarka muke rayuwa, da yardarka kuma muke kwantawa barci, da yardarka kuma muke tashi mu ci gaba da rayuwa.) Idan kuma ya maraita, sai ya ce: ““Alláhumma bika amsainá, wa bika asbahná, wa bika nahyá, wa bika namútu, wa ilaikan- nushúr.” (Ya Ubangiji! Da yardarka muka maraita, da yardarka kuma muka wayi gari. Da yardarka muke rayuwa, da yardarka kuma muke kwantawa barci, a wurinka ne kuma makoma take.) [Abu Dawuda:5068/ Tirmizi:3391], Nawawi kuma ya riwaito shi a cikin: Sunanul- Kubrah: 9836/ Ibn Majah:3868], Ibn Báz kuma rahimahullahu ya inganta danganensa.
1 Sau Da Yawa
اللَّهُمَّ فَاطِرَ السَّمَوَاتِ وَالْأَرْضِ، عَالِمَ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ، لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ رَبَّ كُلِّ شَيْءٍ وَمَلِيكَهُ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ نَفْسِي وَمِنْ شَرِّ الشَّيْطَانِ وَشِرْكِهِ، وَأَنْ أَقْتَرِفَ عَلَى نَفْسِي سُوءًا، أَوْ أَجُرَّهُ إِلَى مُسْلِمٍ
“Alláhumma fáxirus- samáwáti wal- ardhi, álimul- gaibi wash- shahádati, lá’iláha illáh anta, Rabba kulli shai’in wa malíkuhú. A’úzu bika min sharri nafsí, wa min sharrish- shaixáni wa shirkihí, wa an aqtarifa alá nafsí sú’an, au ajurruhú ilá muslimin.” (Ya Ubangiji! Mahaliccin sammai da qasa, Masanin abin duk da yake voye da bayyane. Babu wani abin bautawa da gaskiya sai kai. Ya Ubangijin kowa da komai, kuma mamallakinsa. Ina neman tsarinka daga sharrin kaina, da kuma sharrin Shaixan da ‘yan kazaginsa. Ka kuma tsare ni daga in jefa kaina cikin fitina, ko in jefa wani musulmi a cikinta.) Annabi sallallahu alaihi wa sallam: “Ka yi qoqarin karanta wannan addu’a a duk lokacin da ka wayi gari ko ka maraita, da lokacin da za ka kwanta bacci.” (Imamu Ahmad:6597/ Abu Dawuda:5076/ Tirmizi:3529/ Nisa’i:6799), Malam Ibn Báz rahimahullahu kuma ya inganta shi.
3 Sau Da Yawa
بِسْمِ اللَّهِ الَّذِي لَا يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الْأَرْضِ وَلَا فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
“Babu wani bawa na Allah da zai buxi baki a duk lokacin da aka wayi gari ko aka maraita, ko aka shiga duhun dare; ya karanta: “Bismilláhi’- lazí lá yadhurru ma’as- mihí shai’un fil- ardhi walá fis- samá’i, wa huwas- samí’ul- a lim.” (Ya Ina farawa da sunan Allah, Sarkin da matuqar ana tare da cikakken imani da shi a zuci, babu abin da zai iya haifar da wata cuta, a cikin qasa ko a cikin sama. Shi mai ji ne, mai kuma gani.) Babu wanda zai karanta wannan addu’a qafa uku, face Allah Maxaukakin Sarki ya shiga tsakaninsa da kowace irin cuta.” (Ahmad:446. Tirmizi:110179/ Ibn Majah: 3869), Malam Ibn Báz rahimahullahu kuma ya ce: “Tirmizi ya ce: Wannan hadisi ne kyakkyawa kuma ingantacce.” (lalle ina jin waxannan su ne kalmomin day a yi amfani da su.)
3 Sau Da Yawa
رَضِيتُ بِاللَّهِ رَبًّا، وَبِالْإِسْلَامِ دِينًا، وَبِمُحَمَّدٍ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نَبِيًّا
“Babu wani bawa musulmi da idan aka wayi gari, ko aka maraita, zai karanta qafa uku ta wannan addu’a: Radhítu billáhi Rabban, wa bil’Islámi dínan, wa bi Muhammadin sallallahu alaihi wa sallam Rasúlan wa Nabiyyan.” (Na yarda da Allah shi ne Ubangijina, Musulunci kuma shi ne addinina, Muhammadu sallallahu alaihi wa sallam kuma, shi ne Annabina). Babu wanda zai karanta wannan du’a’i face ya sami haqqin yarda da amincewa daga Allah Maxaukakin Sarki gobe Qiyama.” (Imamu Ahmad:18967/ Tirmizi:3389/ Ibn Majah:3870), Malam Ibn Báz kuma ya kyautata danganensa.
1 Sau Da Yawa
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْعَافِيَةَ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْعَفْوَ وَالْعَافِيَةَ فِي دِينِي وَدُنْيَايَ، وَأَهْلِي وَمَالِي، اللَّهُمَّ اسْتُرْ عَوْرَاتِي، وَآمِنْ رَوْعَاتِي، اللَّهُمَّ احْفَظْنِي مِنْ بَيْنِ يَدَيَّ وَمِنْ خَلْفِي، وَعَنْ يَمِينِي وَعَنْ شِمَالِي، وَمِنْ فَوْقِي، وَأَعُوذُ بِعَظَمَتِكَ أَنْ أُغْتَالَ مِنْ تَحْتِي
“Alláhumma as’alukal- áfiyata fid- duniya wal- ákhirati. Alláhummas- tur aurátí, wa ámin rauátí. Alláhummah- tazní min baini yadayya, wa min khalfí, wa an yamíní, wa an shimálí, wa min fauqí, wa a’úzu bi’azmatika an ugtála min tahtí.” (Ya Ubangiji! Ina roqon ka nasara a cikin al’amurrana na duniya da na lahira. Ya Ubangiji! Ka rufa mani asiri, ka amintar da fargabana. Ya Ubangiji! Ka saka mani gambun tsari a gaba gare ni da kuma baya gare ni, da dama gare ni da kuma hagu gare ni, da kuma birbishina. Ina kuma neman tsari da griman daraja da xaukakarka, daga a yi mini yankan baya.). (Imamu ahmad a cikin: Almusnad:4785/ Abu dawuda5074/ Nasa’ai a cikin: Alkubrá:10401/ Ibn Majah:3871), Hakim kuma ya inganta shi.
3 Sau Da Yawa
أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ
“A’úzu bi kalimátillahi tammati min sharri má khalaqa.” (Ina neman tsari da mafaka qarqashin kalmominka ya Allah cikakki, daga sharrin duk abin da ka halitta.) (Ahmad:7898/ Tirmizi:3437), daga cikin Hadisan Abu Hurairah raliyallahu anhu, Ibn Báz rahimahullahu kuma ya inganta danganensa.
1 Sau Da Yawa
أَمْسَيْنَا عَلَى فِطْرَةِ الْإِسْلَامِ، وَكَلِمَةِ الْإِخْلَاصِ، وَدِينِ نَبِيِّنَا مُحَمَّدٍ - صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - وَمِلَّةِ أَبِينَا إِبْرَاهِيمَ حَنِيفًا, وَمَا كَانَ مِنْ الْمُشْرِكِينَ
Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kasance duk lokacin day a wayi gari yana karanta: “Asbahná alá fixratil- Islámi, wa kalimatil’ ikhlási, wa díni Muhamadin sallallahu alaihi wa sallam, wa millati abíná Ibráhima hanífan, wamá kána minal- mushirikína.” (Mun wayi gari bisa ingantattar aqidarmu ta azaliyya, wato, Musulunci, da lafuzzan bauta wa Allah Maxaukakin Sarki da zuciya xaya, bisa karantarwar addinin Annabinmu Muhammadu sallallahu alaihi wa sallam, da aqidar Annabinmu Ibrahima, wanda bai tava haxa Allah Maxaukakin sarki da wani abu a cikin bauta ba, bai kuma kasance daga cikin mushiriksi ba.) [Ahmad:15367,21144]. Idan kuma ya maraita, sai yakan ce: “Amsainá alá fixratil Islámi……” (Mun maraita bisa ingantattar aqidarmu ta azaliyya, wato, Musulunci,) Ibn Báz rahimahullahu kuma ya inganta danganensa.
1 Sau Da Yawa
يَا حَيُّ يَا قَيُّومُ بِرَحْمَتِكَ أَسْتَغِيثُ أَصْلِحْ لِي شَأْنِي كُلَّهُ، وَلَا تَكِلْنِي إِلَى نَفْسِي طَرْفَةَ عَيْنٍ
“Yá hayyu yá Qayyúmu, bi rahmatika astagísu, aslih lí sha’aní kullahú, walá takilní ilá nafsí xarfata ainin.” (Nisa’i:10405/ Bazzar:2/282), Malam Ibn Hajar kuma da Albani sun kyautata shi. domin qarin bayani sai a duba: Natá’ijul- Afkár:177I da kuma: Silsilatul- Ahádísus- Sahíhah:1/449).
7 Sau Da Yawa
حَسْبِيَ الله لاَ إِلهَ إِلاَّ هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلتُ وَهُوَ رَبُّ الْعَرشِ الْعَظِيمِ
“Hasbiyalláhu lá iláha illá Huwa, alaihi tawakkaltu wa Huwa Rabbul- Arshil- azim.” (Allah ya wadace ni. Babu wani abin bauta da gaskiya sai shi. Gare shi na dogara, shi ne kuma Ubangijin Al’arshin nan gagara misali.) Duk wanda ya karanta wannan addu’a qafa bakwai, Allah zai yaye masa duk baqin cikin da yake damunsa. (Abu dawuda:508), daga cikin Hadisan Abud- Dardái raliyallahu anhu. Sai dai a mafi karvuwar zance a wurin Malaman Hadisi, wannan Hadisi Mauqúfi ne. Amma, gaba xayan mazajensa amintattu ne. Sai dai kuma hukuncincu xaya da Mafú’í kamar yadda Albani ya faxa a cikin: As-silsilá:1/449)