languageIcon
search
search
brightness_1 Caccanza yanayin yatsu

A Sunna, an fi so mutum ya riqa yi yana caccanza yanayin yadda yake xora yatsunsa a kan guwai a lokacin da yake yin “tahiyáh”  tsakanin sifofi guda biyu, da aka riwaito a Sunna.

Sifa ta xaya: A wannan sifa mutum zai rumqe gaba xayan yatsun nasa ne, na hannun dama. Sa’annan ya tayar da manuni tsaye yana kallon alqibla. Shi kuwa hannun dama da yatsunsa, suna can shimfixe a kan guiwar qafarsa ta hagu.

Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin xan Umar raliyallahu anhuma, wanda ya gabata, cewa: “… Annabi sallallahu alaihi wa sallam yana ruqe gaba xayan yatsun hannunsa na dama ne, sa’annan ya tayar da manuninsa, yatsan da yake kusa da babban yatsa, sama yana kallon alqibla…” (Muslimu:580).

Sifa ta biyu: A wannan sifa kuma. Mutum zai qulla hoton wani abu ne mai kama da hamsin da uku a lissafi, ta hanyar rumqe qaramin yatsansa da wanda yake bi masa. Sa’annan ya riqa mommotsa babban yatsa tare da na tsakiya. A yayin das hi kuwa manuni, zai tayar das hi tsaye yana kallon alqibla. Shi kuwa hannun hagu yana can shimfixe a kan guiwar hagu.

Hujja a kan wannan Sunna ita ce, Hadisin can na xan Umar raliyallahu anhu wanda ya gabata, wanda a cikinsa yake cewa: “Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya kasance, idan ya zauna zai yi “tahiyáh” yakan xora hannunsa na hagu a kan qafarsa ta hagu. Hannunsa na dama kuma, sai ya xora shi a kan qafarsa ta dama. Sa’annan ya qulla hoton talatin da biyar ta lissafi. Manuninsa kuma, sai ya tayar da shi sama yana kallon alqibla.” (Muslimu:850).

 

brightness_1 Caccanza sigogin “tahiyáh”

Sunna ce ga mutum ya riqa caccanza sigogin “tahiyáh”  waxanda aka riwaito a Sunna; isan ya yi wannan yau, gobe kuma ya yi waccan. Daga cikin waxannan sigogi akwai:

a) “Attahiyyátu lilláhi, was- salawátu, wax- xayyibátu, assalámu alaika ayyuhan- Nabiyyu wa rahamatulláhi wa barakátuhu. Assalámu alainá wa alá ibádilláhis- sálihína. Ash- hadu allá’iláha illalláhu, wa ash- hadu anna Muhammadan Abduhú wa Rasuluhú.” (Tsarkakan kalmomin gaisuwa, da salati, sun tabbata ga Allah. Aminci kuma, da rahamar Allah da albarkarsa, su tabbata gare ka ya kai wannan Annabi. Muma aminci ya tabbata a gare mu, da kuma ga sauran bayin Allah na qwarai. Ana shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Ina kuma shaida cewa, lalle Muhammadu Bawansa ne kuma Manzonsa ). [Buhari:1202/ Muslimu:402], daga cikin Hadisan xan Mas’ud raliyallahu anhu.

b) a) “Attahiyyátul- mubárakátu,  was- salawátux- xayyibátu lilláhi. Assalámu alaika ayyuhan- Nabiyyu…” (Tsarkakkakn kalmomin gaisuwa masu albarka, da salati, sun tabbata ga Allah. Aminci kuma ya tabbata gare ka ya kai wannan Annabi….). Sai kuma a cika har qarshe kamar yadda yake a sama.  [Muslimu:403] daga cikin Hadisan xan Abbas raliyallahu anhuma  

c) a) “Attahiyyátux- xayyibátus- saláwátu lilláhi. Aassalámu alaika ayyuhan- Nabiyyu….” (Tsarkakan kalmomin gaisuwa da salati, sun tabbata ga Allah. Aminci kuma, ya tabbata gare ka ya kai wannan Annabi…) Sai kuma a cika har qarshe kamar yadda yake a can farko. (Muslimu404), daga cikin Hadisan Abu Musa raliyallahu anhu.  

brightness_1 Caccanza salati ga Annabi sallallahu alaihi wa sallam

Sunna ce mutum ya riqa yi yana kaiwa da komwa a tsakanin sigogin salati ga Annabi sallallahu alaihi wa salla, da aka riwaito; idan ya yi wannan yau, gobe ya yi wancan. Daga cikin waxannan sigogi akwai:

a) Alláhumma salli alá Muhammadin, wa alá áli Muhammadin, kamá sallaita alá Ibrahíma, wa alá áli Ibráhima innaka hamídun Majídun. Alláhumma bárik alá áli Muhammadin, kamá bárakta alá Ibráhíma. Innaka Hamídun Majid. (Ya Ubangiji! Ka daxa tsira ga Annabi Muhammadu, da alayen Annabi Muhammadu, kamar yadda ka yi tsira ga Annabi Ibrahima da alayen Annabi Ibrahima. Lalle kai abin godiya ne, abin kuma giramamawa. Ya Ubangiji! Ka daxa aminci  ga Annabi Muhammadu, da alayen Annabi Muhammadu, kamar yadda ka daxa aminci ga Annabi Ibrahima da alayen Annabi Ibrahima. Lalle kai abin godiya ne, abin kuma giramamawa.) [Buhari:3370] daga cikin Hadisan Ka’abu xan Ujrah raliyallahu anhu.

b) Alláhumma salli alá Muhammadin, wa alá áli Muhammadin, kamá sallaita alá áli Ibráhima. Wa bárik alá Muhammadin wa alá áli Muhammadin, kamá bárakta alá áli Ibráhíma, fil álamína Innaka Hamídun Majid. (Ya Ubangiji! Ka daxa tsira ga Annabi Muhammadu, da alayen Annabi Muhammadu, kamar yadda ka yi tsira ga alayen Annabi Ibrahima. Ka kuma yi albarka ga Annabi Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka  ga alayen Annabi Ibrahima, a cikin talikai. Lalle kai abin godiya ne, abin kuma giramamawa.) [Muslimu:305] daga cikin Hadisan Abu Ms’ud Al- Ansárí raliyallahu anhu.

a) Alláhumma salli alá Muhammadin, wa alá azwájihí wa zurriyátihí, kamá sallaita alá áli Ibrahíma,  wa bárik alá áli Muhammadin, wa alá azwájihí wa zurriyátihí, kamá bárakta alá áli Ibráhíma. Innaka Hamídun Majid. (Ya Ubangiji! Ka daxa tsira ga Annabi Muhammadu, da matansa da zuri’arsa,  kamar yadda ka yi tsira ga  alayen Annabi Ibrahima. Ka kuma yi albarka  ga Annabi Muhammadu, da matansa da zuri’arsa   kamar yadda ka yi albarka ga alayen Annabi Ibrahima. Lalle kai abin godiya ne, abin kuma giramamawa.) [Buhari:3369/ Muslimu:407] daga cikin Hadisan Abu Humaidin As- Sá’idí raliyallahu anhu.

 

brightness_1 Akwai kuma waxansu addu’o’in na daban da suka Sunna ta zo da su

Akwai kuma waxansu addu’o’in na daban da suka Sunna ta zo da su, waxanda ba waxannan ba, da take kuma da bukatar mai salla ya riqa caccanza hannu a tsakaninsu, kafin ya sallame sallarsa. Daga cikinsu akwai:

1/ “Alláhumma inní a’uzu bika minal- ma’asami wal- magrami.” (Ya Ubangiji! Ina roqon tsarika daga ayyukan savo da na zunubi.) (Buhari:832/ Muslimu:589)..

2/ “Alláhumma inní as’alukal- Jannata wa aúzu bika minan- Nári.” (Ya Ubangiji! Ina roqon ka sadakar Aljanna, ina kuma neman tsarinka daga Wuta.) [Abu Dawuda:792] Albani kuma ya inganta danganensa: (Sahíhu Abi Dawuda:3/377).

3/ “Alláhumma inná zalamtu nafsí zulman kasíran, wa lá iagfiruz- zuna illá anta. Fagfir lí magfiratan min indika, war- hamná, innaka antal- Gafúrur- Rahím.” (Ya Ubangiji! Na zalunci kaina, zalunci mai yawa, babu kuma mai gafarar zunubai sai kai. Ka gafarta mani, gafara ta musamman daga wajjenka, ka kuma yi mani rahama. lalle kai, mai yawan gafara ne, mai kuma yawan jinqayi.) [Buhari:6326/ Muslimu:2705].

4/ “Alláhumma a’inní alá zikrika, wa shukrika, wa husni ibádatika.” (Ya Ubangiji! Ka taimake ni in riqa ambatonka, in riqa kuma godiya a gare ka, sa’annan in rika kyautata bautarka.) [Ahmad:22119/ Abu Dawuda:522/ Nasa’i:1304[, Albani kuma ya ainganta shi: (Sahíhul- Jámi’i:2/1320).

5/ “Alláhumma inní a’úzu bika minal- bukhuli, wa a’úzu bika minal- jubuni, wa a’úzu bika an uradda ilá arzalil- umri, wa a’úzu bika min fitnatid- duniya, wa a’úzu bika min azábil qabri.” (Ya Ubangiji! Ina neman tsarinka daga sharrin rowa, ina kuma neman tsarinka daga zama matsoraci, ina kuma neman tsarinka daga a mayar da ni zuwa mafi qasqancin shekaru, ina kuma neman tsarinka daga fitinonin xakin duniya, ina kuma neman tsarinka daga azabar qabari.) [Buhari:6370].

6/ “Alláhumma hásibní hisában yasírá.” (Ya Ubangiji! Ina roqon ka yi mani hisabi mai sauqi.) [Ahmad:24215] Albani kuma ya inganta shi a cikin: ‘Tahqiqu mishkátul- Masábíh:3/1544

Daga nan daxa, sai mutum ya sallame sallarsa ta hanyar yuja kansa. juya kai domin sallama Sunna ne. haka nan kaiwa matuqa a cikin juyawa xin, shi ma Sunna ne. dalili kuwa shi ne, irin yadda ta tabbata cewa, Annabi sallallahu alaihi wa sallam yakan juya kansa sosai domin sallam har sai an hango kaye-kayin kundukukinsa daga bayansa, sallallahu alaihi wa sallam. Hujja a kan wannan Sunna kuwa ita ce, Hadisin da aka riwaito daga Sa’ad xan Abi Waqqas raliyallahu anhu, inda ya ce: “Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya kasance yana juya kansa dama da hagu domin yin sallama, har in hangi katekayin kundukukinsa.” (Muslimu:582).